‘Yan bindiga sun kashe mutane 2 da sace 50 a Kaduna

66

An kashe mutane biyu tare da yin garkuwa da sama da mutane 50 bayan wasu ‘yan bindiga sun kai hari a Ungwan Gimbiya da ke Sabo a karamar hukumar Chikun ta jihar Kaduna.

An rawaito cewa ’yan bindigar dauke da makamai, wadanda suka zo da yawansu da sanyin safiyar yau, sun dauki kimanin sa’o’i biyu suna shiga gida bayan gida domin neman wadanda abin ya shafa.

Wani mazaunin yankin mai suna Gideon Jatau, wanda ya tabbatar da faruwar harin, ya ce mazauna yankin ba su taba samun irin wannan mummunan abu ba.

Ya yi zargin cewa mutane dayawa sun yi gudun hijira zuwa wurare masu tsaro saboda fargabar sake kai wani harin.

Da aka tuntubi jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna, ASP Mohammed Jalige, ya yi alkawarin zai sake kira amma bai kira ba har zuwa lokacin hada wannan rahoto.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

four × four =