
Wasu ‘yan bindiga sun kai hari a wani masallaci a garin Tella da ke karamar hukumar Gassol a jihar Taraba, inda suka yi awon gaba da wasu mutane hudu.
Wani mazaunin garin Tella, Suleiman Rabiu, ya shaida wa manema labarai cewa ‘yan bindigar kimanin su 12, sun kewaye masallacin tare da yin awon gaba da masu ibada da suke sallar isha’i.
Majiyar ta ce ‘yan bindigar bayan sun katse sallar sai suka fitar da masallatan daga Masallacin ta hanyar razana su da bindiga.
Majiyar ta kara da cewa daga bisani ‘yan bindigar sun sako mutum guda tare da kai sauran inda ba a san ko ina ne ba.
Daga cikin wadanda aka sace akwai Alhaji Yahaya da Aminu Dali da kuma Alhaji Hussaini wanda shi ne shugaban dillalan hatsi a yankin.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Taraba Usman Abdullahi ya tabbatar da faruwar lamarin a masallacin amma bai yi cikakken bayani ba.