Shirin Abinci na MDD ya dakatar da rabon abinci a Habasha

46

Shirin samar da abinci na Majalisar Dinkin Duniya, ya dakatar da raba kayan agaji a garuruwa biyu da ke arewacin kasar Habasha bayan ‘yan bindiga sun sace kayan.

Majalisar Dinkin Duniya ta ce barayin da ke yankin da mayakan Tigray ke iko da shi, sun rutsa ma’aikatan agaji biyu da ‘yan bindiga a garin Kombolcha.

Sun sace kayan abinci masu tarin yawa, ciki har da wanda aka yi domin bai wa kananan yara mai gina jiki.

Arewacin Habasha na fuskantar matsananciyar yunwa, sakamakon cigaba da gwabza fada tsakanin dakarun gwamnati da na ‘yan tawayen Tigray.

Bayan shafe shekara guda ana fadan, Majalisar Dinkin Duniya ta ce sama da mutane miliyan 9 ne ke tsananin bukatar abinci a kasar.

Kakakin majalisar dinkin duniyar yace ma’aikatansu na fuskantar barazana.

Kakakin ya kuma zargi jami’an soji da kwace manyan motoci na shirin samar da abinci kuma suke amfani da su domin ayyukansu.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

three + ten =