Osinbajo ya jagoranci zaman majalisar zartarwa ta kasa na musamman

8

Mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo a yau ya jagoranci wani taro na musamman na majalisar zartarwa ta tarayya a fadar shugaban kasa dake Abuja.

Taron dai an gudanar da shi ne a cikin wani salo na zamani a zauren majalisar zartarwa ta fadar shugaban kasa.

Ministocin da suka halarci taron sun hada da ministan yada labarai da al’adu, Lai Mohammed, ministan shari’a kuma babban lauyan tarayya, Abubakar Malami, ministar kudi, kasafin kudi da tsare-tsare na kasa, Zainab Ahmed, ministan sufurin jiragen sama, Hadi Sirika da ministan albarkatun ruwa, Suleiman Adamu.

Sakataren gwamnatin tarayya Boss Mustapha da mataimakin shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, Ade Ipaye da sauransu suma sun halarci taron.

A zamanta na jiya, Majalisar zartaswa ta tarayya ta amince da kudi naira miliyan dubu 5 da miliyan 700 domin gudanar da ayyukan samar da ruwan sha guda biyu a jihar Yobe da kuma sayen iri na amfanin gona daban-daban domin bunkasa noman abinci a kasar nan.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

eight + 3 =