Na jajirce wajen inganta rayuwar talakan Najeriya – Buhari

10

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi kira ga ‘yan Najeriya da su sake farfado da fata nagari a kasarnan, inda ya bukace su da su yi amfani da lokacin Kirsimeti wajen nuna soyayya ga juna.

A sakonsa na Kirsimeti a yau, Buhari ya ce ya kamata ‘yan Najeriya su yi amfani da lokacin bukukuwan don karfafa wa juna gwiwa, ta yadda makircin miyagu ba zai samu gindin zama ba.

Shugaba Buhari ya ce gwamnatinsa ta tsaya tsayin daka wajen ganin an daukaka darajar rayuwar talakawan Najeriya.

Akan yaki da rashin tsaro, shugaba Buhari ya ba da tabbacin cewa da sabbin alkawurran da hukumomin tsaro suka dauka, nan ba da jimawa ba ‘yan Najeriya za su samu cigaba.

A cewar sa, gwamnatinsa na ci gaba da tallafawa jami’an tsaro wajen gudanar da ayyukansu.

Ya kuma yi amfani da sakon wajen yin kira ga dukkan ‘yan Najeriya da su yi allurar rigakafin cutar corona.

A wani labarin kuma, tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar, ya bukaci ‘yan Najeriya da su kasance masu niyya wajen yin tunani mai kyau da kuma assasa ingantacciyar alaka da hadin kai.

Atiku Abubakar, a cikin sakonsa na Kirsimeti da ofishinsa na yada labarai ya fitar yau a Abuja, ya ce ayyukan za su kara daukaka Najeriya a yau da kuma nan gaba.

Ya ce yayin da duniya ke bukukuwan Kirsimeti, wanda bikine na murnar haihuwar Yesu Almasihu, ya kamata ‘yan Najeriya su rungumi zaman lafiya da hadin kai a wannan lokaci.

Tsohon mataimakin shugaban kasar ya bukaci ‘yan Najeriya da su so junansu domin samun ci gaba da daukakar kasarnan.

Tsohon mataimakin shugaban kasar ya tunatar da ‘yan Najeriya cewa farfado da martabar kasar alhakine da ya rataya a wuyan kowa da kowa.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

5 + eighteen =