Ana fargabar yawancin fasinjoji kusan 50 da ke cikin kwale-kwale sun mutu bayan da kwale-kwalen ya kife a yammacin jiya a kogin Bagwai da ke karamar hukumar Bagwai a jihar Kano.
Daga cikin fasinjojin har da daliban makarantar islamiyya da suke zuwa wani taron mauludi a hedikwatar karamar hukumar.
Kakakin ‘yan sanda a Kano, Abdullahi Kiyawa, ya shaida wa manema labarai cewa, an ceto bakwai daga cikin fasinjojin da ke cikin kwale-kwalen bayan hadarin amma sauran ba a gansu ba.
Abdullahi Kiyawa bai bada adadin fasinjojin da ke cikin kwale-kwalen ba.
Rahotanni sun bayyana cewa wadanda abin ya shafa na kan hanyarsu ta zuwa karamar hukumar Tofa domin ci gaba da gudanar da bukukuwan Mauludi.
A halin da ake ciki, jami’ai sun tabbatar da cewa an gano gawarwaki 29 a lamarin.
Ana ci gaba da gudanar da aikin bincike da ceto wanda ya hada da ‘yan sanda, hukumar kashe gobara da ‘yan civil defence da kuma ‘yan sa kai.