Majalisar wakilai ta zartar da kasafin kudin 2022

14

Majalisar wakilai a yau ta zartar da kiyasin kasafin kudin badi tare da karin farashin danyen man fetur daga dala 57 zuwa dala 62 kowacce ganga.

Karin farashin na man fetur ya jawo kasafin kudin ya karu zuwa naira tiriliyan 17 da biliyan 120 daga naira tiriliyan 16 da biliyan 390 da bangaren zartarwa ya gabatar.

An zartar da kasafin ne a yau bayan amincewa da rahoton kwamitin kasafin kudi na majalisar wanda shugaban kwamitin Mukhtar Batera ya mika.

A cewar rahoton na Betara, za a raba karin kudaden shiga ga hukumomin da suka gabatar da bukatun karin neman kudaden da ba a shigar a baya ba.

Wadannan hukumomin sun hada da Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) don zaben 2023 da Ma’aikatar Ayyuka da Gidaje ta Tarayya da majalisar kasa saboda ayyukan mazabu da Ma’aikatar Albarkatun Ruwa ta Tarayya da Hukumar Kidayar Jama’a ta Kasa don aikin kidayar jama’a a shekara mai zuwa.

A halin da ake ciki, Majalisar Dattawa ta amince da bukatar shugaban kasa Muhammadu Buhari na kara wa’adin fara aiwatar da kasafin kudin badi daga watan Disambar da muke ciki zuwa watan Maris na badi.

Bukatar shugaban kasar na kunshe ne a cikin wata wasika zuwa ga shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan, wanda ya karanta ta a farkon zaman majalisar na yau.

A cikin wasikar, Buhari ya ce ya nemi a kara wa’adin fara aiwatar da kasafin kudin badi har zuwa watan Maris na badi saboda gwamnatin tarayya na neman samar da kudaden aiwatar da muhimman bukatu na gaggawa da aka tanada a cikin kudirin kasafin kudin.

Buhari ya ce bukatarsa ​​ta neman karin wa’adin za ta inganta kokarin gwamnatin tarayya na inganta rayuwar ‘yan Najeriya.

Jim kadan bayan karanta wasikar shugaban kasar, ‘yan majalisar sun yi gaggawar gyara dokar kasafin kudin domin biyan bukatarsa.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

five × four =