Gwamnati tace ‘yan Najeriya zasu fara biyan karin haraji

21

Ministar Kudi, Kasafin Kudi da Tsare-Tsaren Kasa, Zainab Ahmed ta ce ‘yan Najeriya za su fara biyan sabon kudin haraji nan gaba.

Da take magana a jiya yayin taron jin ra’ayin jama’a kan Kudirin Dokar Kudi ta bana, Zainab Ahmed ta fadawa kwamatin kudi na Majalisar Wakilai cewa matakin na kunshe ne cikin dokar.

Sai dai ta fadawa wata kafar yada labarai cewa ya yi wuri a fayyace sashen da za a kara wa harajin, ko dai a kan harajin sayen kayayyakin yau da kullum na VAT ko kuma harajin shigo da kaya. Ta kara da cewa wajibi ne gwamnatin tarayya ta fadada hanyoyin samun kudadenta daga man fetur domin gudanar da manyan ayyuka.

Da yake bude taro da jawabi, kakakin majalisar, Femi Gbajabiamila, wanda ya samu wakilcin shugaban marasa rinjaye na majalisar, Ndudi Elumelu, yace kudirin dokar kudi ta bana na kokarin kawo sauye-sauye masu ma’ana wadanda zasu kula da ciyo bashi daga gwamnatin tarayya da jihoshi da kananan hukumomi.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

nineteen − 15 =