Gwamnati ta ce ‘yan Najeriya miliyan 109 zasu talauce nan da 2022

7

Gwamnatin tarayya a jiya tace adadin talakawan kasarnan zasu karu zuwa kimanin miliyan 109 a karshen shekara mai zuwa.

Ministar Kudi, Kasafin Kudi da Tsare-Tsaren Kasa, Zainab Ahmed, ta ce akwai yiyuwar ‘yan Najeriya miliyan 11 za su fada kangin talauci a karshen shekarar 2022 sakamakon annobar corona.

Ta yi magana a Abuja a yayin taron corona na kasa da ake gudanarwa.

Ministar wacce Darakta Janar na ofishin kasafin kudi, Ben Akabueze ya wakilta, ya ce kafin barkewar cutar, ana tsammanin kimanin ‘yan Najeriya miliyan biyu za su fada kangin talauci nan da shekarar 2020, yayin da karuwar al’umma ta zarce ci gaban tattalin arziki.

Ta ce sanadiyyar corona, koma bayan tattalin arziki ya tura karin ‘yan Najeriya miliyan 6.6 kangin talauci a shekarar 2020, wanda ya kara sabbin matalauta zuwa miliyan 8 a dubu 600 a shekarar.

Ta ambaci rashin aikin yi da samun raguwar kudaden shiga a hannun mutane, a matsayin abubuwan dake kara talauci.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

four + 10 =