Buhari zai sanya hannu kan kasafin kudin badi ranar Juma’a

4

Ana sa ran Shugaban Kasa Muhammadu zai sanya hannu akan kasafin kudin badi a ranar Juma’a mai zuwa, 31 ga watan Disambar da muke ciki.

Hakan ya biyo bayan aikawa da kudirin kasafin kudi da aka sanyawa daga majisun kasa.

Wata majiya a ofishin akawun majalisar kasa ta tabbatar da cewa an aika da kasafin kudin ga shugaban kasar.

Majiyar ta musanta rahoton dake cewa ba a aika da kasafin kudin zuwa ga shugaban kasa ba, kwanaki 3 kafin shekarar ta kare.

Majalisar wakilai da ta dattawa sun zartar da kasafin kudin badi a makon da ya gabata, kafin su tafi hutunsu na shekara-shekara.

A wani labarin kuma, ministan shari’ah kuma babban lauyan tarayya, Abubakar Malami, yace kudirin dokar zaben da aka gyara na agazawa rashin tsaro da nuna wariya shiyasa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ki sanya hannu.

Ministan, wanda ya sanar da wannan matsayar tasa a wani shirin kiran waya na Radio Kano, ya kuma kafe kan cewa kudirin dokar zaben zata haifar da kashe kudade dayawa, shiyasa shugaban kasar ya ki sanya hannu akai.

A cewarsa, sabuwar dokar zaben bata kula da bukatun dukkan ‘yan Najeriya ba, inda ya kara da cewa sanya mata hannu daga Shugaban Kasar zai haifar da karin rikici a dandalin siyasa.

A cewar Minsitan, ‘yan majalisar na kare muradunsu ne kadai, yayin da shugaban kasa yake kula da rayuwar dukkan ‘yan Najeriya, ‘yan siyasa da wadanda ba ‘yan siyasa ba.

Yace duk wani kudirin doka da shugaban kasa zai sanyawa hannu, zai kula da bukatun dukkan ‘yan Najeriya.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

thirteen + 18 =