Buhari ya kaddamar da sashe na 3 na titin Kano-Maidugri

64

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari a yau ya kaddamar da titi mai nisan kilomita 106.341 akan hanyar Kano zuwa Maiduguri, sashe na uku na Azare zuwa Postisum da ya hada jihoshin Bauchi da Yobe.

Kamfanin dillancin labarai na kasa ya bayar da rahoton cewa Shugaban Kasar ya kaddamar da sashen na uku da aka kammala a garin Azare, helkwatar karamar hukumar Katagum a jihar Bauchi.

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, wanda ya samu wakilcin karamin ministan masana’antu, kasuwanci da zuba jari, Ambassada Maryam Yalwaji Katagum, yace aikin wani bangare ne na jajircewar gwamnatinsa wajen samar da tituna masu inganci a kasarnan.

Shugaba Buhari ya hori masu ababen hawa da sauran masu amfani da tituna da su tabbatar da sun yi amfani da titin ta hanyar da ta dace, tare da tsare shi, da kuma bayar da rahoton lalacewarsa ga hukumomin da suka kamata.

A nasa jawabin, ministan ayyuka da gidaje, Babatunde Raji Fashola, yace titin zai hada jihoshin Bauchi da Yobe, inda ya kara da cewa zai habaka cigaban hada-hadar tattalin arziki.

A wani labarin kuma, Shugaban Kasa Muhammadu Buhari da Mai Alfarma Sarkin Musulmai, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar, da tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo da tsohon shugaban kasa na mulkin soja Abdulsalami Abubakar, sun aza harsashin ginin cibiyar binciken dangantaka tsakanin Kiristoci da Musulmai ta Kaduna.

Cibiyar za ta tabbatar da fahimtar juna, kyakyawar dangantaka da hadin kai da tallafawa juna da nufin dabbaka zaman lafiya tsakanin mabiya addinan biyu.

Da yake jawabi yayin bikin aza harsashin cibiyar jiya a Kaduna, Shugaba Buhari yace rikicin addini tsawon shekaru ya haifar da wahalhalu da rashin yarda da juna tsakanin ‘yan Najeriya, inda ya tabbatar da cewa cibiyar za ta samun tallafin gwamnati.

Shugaban Kasar wanda ya samu wakilcin Karamin ministan ilimi, Chukwuemeka Nwajiuba, yace cibiyar zata kasance harsashin samar da zaman lafiya kuma kammaluwarta na bukatar juriya, jajircewa da sadaukar da kai.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

3 × 1 =