Buhari ya bayyana goyon baya ga matan Najeriya

2

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya bayar da tabbacin cewa ‘yan Najeriya ba za su kara yin jimami da alhinin asarar rayukan da aka samu sakamakon rashin tsaro a kasarnan ba.

Shugaban kasar ya ba da wannan tabbacin ne a lokacin da yake jajantawa iyalan ‘yan sandan da aka ce bata gari sun kashe su a yankin Kudu maso Gabas, tare da daukar bidiyon kisan gillar, sannan kuma suka yada shi a kafafen sada zumunta.

A wata sanarwa da babban mai taimaka masa kan harkokin yada labarai Femi Adesina ya fitar a jiya, shugaban kasar ya koka da yadda ake tafka ta’asa da zubar da jini, inda yace kiyayya ta mamaye zukatan mutane dayawa.

A wani labarin kuma, shugaban kasa Muhammadu Buhari a jiya ya bayyana goyon bayansa ga matan Najeriya yayin da suke bikin kwanaki 16 na fafutukar yaki da cin zarafin mata daga ranar 25 ga Nuwamba zuwa 10 ga Disambar da muke ciki.

Mai taimaka wa shugaban kasa kan harkokin yada labarai, Femi Adesina, ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a Abuja, inda ya ce shugaban ya bayyana goyon bayansa ne a lokacin da ya karbi bakuncin ministar harkokin mata, Pauline Tallen da ta ziyarce shi.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

nineteen − four =