Buhari ya aika da kudirin kudade na bana zuwa majalisa

32

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari jiya a Abuja ya aika da kudirin kudade ga majalisar dattawa domin amincewa.

Shugaban Majalisar Dattawa, Ahmad Lawan, ya karanta wasikar a zauren majalisar ta dattawa yayin zaman yau.

A cewar shugaban kasar, kudirin zai samar da hanyoyin inganta kokarin tattara kudade domin karin haraji da kudaden shigar da ba na haraji ba.

Buhari ya kuma kara neman samar da daftarin yin garanbawul a kula da haraji da nufin tallafawa komawa aiki da na’ura da hukumar tara kudaden shiga ta kasa ke gudanarwa.

Ya kuma nemi a gaggauta garanbawul akan dokokin harajin kasa da kasa domin inganta karbar harajin wadanda ba ‘yan kasa ba da kamfanonin baki, wadanda suke samun riba a Najeriya.

A cewarsa, kudirin ya kuma bukaci aiwatar da garanbawul a bangaren kudade da nufin tallafawa hada-hadar hannayen jari da ta gidaje da inshora da sauransu.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

6 + nine =