Birtaniya ta janye haramcin da ta kakabawa kasashen Africa

19

Birtaniya ta cire dukkan kasashen Afirka 11 daga cikin wadanda ta haramtawa shiga kasarta.

An fara sanya takunkumin ne a watan da ya gabata domin a sassauta yaduwar kwayar cutar corona nau’in Omicron.

Wasu masu sukar lamirin sun bayyana matakin a matsayin na wariyar launin fata ganin cewa kasashen Afirka ne kawai suka shiga cikin jerin kasashen da aka kakabawa haramcin.

Da farko sun kasance a kudancin Afirka, ciki har da Afirka ta Kudu da Botswana, inda aka fara samun nau’in Omicron, amma daga baya aka kara da Najeriya.

Kasashe 11 da abin ya shafa sun hada da; Angola, Botswana, Eswatini, Lesotho, Malawi, Mozambique, Namibia, Najeriya, Afirka ta Kudu, Zambia da Zimbabwe.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

3 × 4 =