Bankin duniya ya shawarci gwamnatin tarayya ta kakaba haraji kan giya

31

Bankin Duniya ya yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta sanya haraji na musamman kan giya da sigari da duk wani abin sha mai zaki domin inganta harkar lafiya a matakin farko.

Darakta mai kula da harkokin bankin duniya a Najeriya Shubham Chaudhuri ne ya yi wannan kiran yau a Abuja a wani taro na musamman na majalisar kula da lafiya ta kasa da ma’aikatar lafiya ta tarayya ta shirya.

Chaudhuri ya lura cewa haraji kan taba, barasa, da abin sha mai zaki zai rage hadarin kiwon lafiya da ke tattare da shan su tare da fadad hanyoyin samar da kudade kasafin kudin kiwon lafiya bayan cutar corona.

Daraktan kasar ya bayyana cewa saka hannun jari a tsarin kiwon lafiya mai karfi ga kowa zai taimaka wajen magance karuwar talauci da rashin daidaito.

Ya kara da cewa karin harajin kiwon lafiya zai kara samar da fa’idar rage kudaden da aka kashewa a kiwon lafiya nan gaba ta hanyar dakile cigaban cututtukan da ba sa yaduwa ta hanayar shan sigari da giya da abubuwan sha masu zaki.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

fourteen − 11 =