ASUU tace babu ja da baya dangane da yajin aiki

19

Kungiyar malaman jami’o’i ta kasa (ASUU) tace naira biliyan 55 da rabi da gwamnatin tarayya ta sakarwa jami’o’i domin cika wani bangare na alkawarin da ta daukarwa kungiyar, baza su isa ba wajen hana tafiya yajin aikin da ta shirya.

Kungiyar, cikin wata sanarwa da aka fitar a karshen zamanta na shiyyar Kudu maso yamma, wanda aka gudanar a jiya a jami’ar aikin gona ta tarayya dake Abeokuta a jihar Ogun, ta bayyana kudaden a matsayin dan kadan bisa la’akari da biliyoyin naira da kungiyar ke nema na gyaran gine-gine da alawus din koyarwa.

Sanarwar, wacce shugaban kungiyar na shiyyar, Adelaja Odukoya, ya sanyawa hannu, yace wani bangare na matakan dakatar da yajin aikin shine gwamnati ta gaggauta kawo karshen IPPIS a jami’o’i kuma ta sanya hannu akan sabuwar yarjejeniyar da aka cimma a watan Mayun 2021.

Sabuwar barazanar na zuwa ne kwanaki 9 daidai bayan kungiyar ta dakatar da dogon yajin aikinta na watanni 9, wanda ya gurgunta harkokin koyo da koyarwa a fadin jami’o’in kasarnan.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

9 + eighteen =