An kashe mutane biyu a rikice-rikicen manoma da makiyaya a Jigawa

52

Rundunar ‘yan sandan jihar Jigawa ta ce akalla mutane biyu ne suka mutu a wani rikici tsakanin manoma da makiyaya a jihar.

Kakakin rundunar ‘yansandan jiharnan, ASP Lawan Shiisu Adam, ya tabbatar da hakan a wata sanarwa da ya raba wa manema labarai.

Ya ce lamarin ya faru ne a karamar hukumar Taura.

Kazalika, Shisu Adam ya kuma bayyana cewa irin wannan lamari ya faru a Gandun Galadima da ke karamar hukumar Malam Madori.

Ya ce a sakamakon faruwar lamarin mutane biyar sun samu raunuka daban-daban kuma an garzaya da su babban asibitin Hadejia domin kula da lafiyarsu.

Ya kara da cewa an tabbatar da mutuwar wani matashi mai suna Yakubu Saleh na Gandun Sarki, dan shekaru 30 a duniya a lokacin da yake jinya a asibiti.

Kakakin ya ce an kama mutane biyar da ake zargi da hannu a lamarin.

A wani labarin kuma, Rundunar ‘yan sandan jihar Jigawa ta kama wasu mutane bakwai lokacin da ta kai farmaki zuwa wajen aikata laifuka da maboyar batagari a kananan hukumomin Birninkudu da Gwaram.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, ASP Lawan Shiisu, ya tabbatar da kamen ga Kamfanin Dillancin Labarai na kasa a yau a Dutse.

Shiisu Adam ya ce uku daga cikin wadanda ake zargin, masu shekaru tsakanin 20 zuwa 28, an kama su ne a kauyen Babaldu da ke karamar hukumar Birninkudu, lokacin da tawagar ‘yan sanda da ke sintiri suka kai farmaki zuwa wajen aikata laifuka da maboyar batagari a garin.

Ya bayyana cewa an samu kunshi 85 na ganyen da ake zargin tabar wiwi ce, da kwayoyi guda 136, da sholisho ga 24, da kuma wuka guda daya a yayin farmakin.

Shiisu Adam ya kara da cewa ana cigaba da gudanar da bincike kafin a gurfanar da wadanda ake zargin a gaban kotu.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

sixteen + 15 =