An kashe kwamishinan kimiyya da fasaha na Katsina

42

An kashe kwamishinan kimiyya da fasaha na jihar Katsina, Dr. Nasir Rabe.

An rawaito cewa wadanda suka kashe shi sun kashe shi ne a gidansa dake rukunin gidaje na Fatima Shema a birnin Katsina, inda suka ja gawarsa suka bandaki suka kulle ta.

Wata majiya tace a jiya aka kashe shi, yayin da wata majiyar tace a yau aka kashe shi. An kuma tattaro cewa shi kadai ne a gidan lokacin da aka kashe shi.

Majiyar tace yaron gidansa ne ya fara jawo hankalin jama’a dangane da kisan bayan yazo gidan ya tarar da jini a kasa yau da rana.

Mamacin a baya shine mai bawa Gwamna Aminu Bello Masari shawara akan kimiyya da fasaha, kafin daga bisani a kara masa girma zuwa kwamishina.

An haife shi a Mani, a karamar hukumar Mani ta jihar Katsina.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

13 + sixteen =