Al-Shabab ta sace daruruwan mata a kasar Mozambique

31

Wani rahoto da kungiyar kare hakkin bil’adama ta Human Rights Watch ta fitar ya ce akalla mata da ‘yan mata 600 ne wasu ‘yan bindiga suka yi garkuwa da su tare da bautar da su cikin shekaru uku da suka gabata a lardin Cabo Delgado da ke arewacin kasar Mozambique.

A cewar rahoton, kungiyar mayakan da ke da alaka da IS da aka fi sani da al-Shabab ta tilastawa ‘yan matan dake tsare a hannunsu masu kyau da farar fata da su auri mayakansu.

An sayar da wasu daga cikin wadanda aka sace ga mayakan kasashen waje, wasu kuma an sake su bayan iyalansu sun biya kudin fansa, yayin da aka sako wasu bayan farmakin da sojoji suka kai karkashin jagorancin dakarun gwamnati da na yankin.

Human Rights Watch ta yi kira ga mayakan da su saki wadanda ake tsare da su.

Kungiyar dake kare hakkin bil adama ta gudanar da binciken nata ne tsakanin watan Augustan 2019 zuwa Oktoban bana kuma binciken nata ya samo asali ne daga hirar da aka yi da wadanda aka taba sacewa a baya, da ‘yan uwansu, da majiyoyin tsaro, da jami’an gwamnati, da kuma rahotannin kafafen yada labarai.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

12 + four =