Akalla mutane 37 sun mutu bayan jirgin ruwa ya kama da wuta a Bangladesh

9

Akalla mutane 37 ne suka mutu yayin da wasu 100 suka jikkata bayan da wani jirgin ruwa ya kama wuta a kudancin Bangladesh.

Wutar jirgin mai hawa uku ya kama da wuta ne ne a tsakiyar kogi kusa da garin Jhalakathi a lokacin da ya taso daga Dhaka babban birnin kasar zuwa garin Barguna.

Wasu daga cikin wadanda abin ya rutsa da su sun nutse bayan da suka shiga dira zuwa cikin ruwa.

Adadin wadanda suka mutu a iftila’in na yau na iya karuwa yayin da yawancin fasinjojin suka samu kuna sosai.

Kimanin mutane 500 ne aka ruwaito suna cikin jirgin.

Jami’in hukumar kashe gobara, Kamal Hossain Bhuiyan, ya shaidawa kafafen yada labarai na cikin gida cewa ana kyautata zaton gobarar ta tashi ne a dakin injin jirgin, kuma cikin sauri ta bazu yayin da jirgin ke tafiya a bakin kogin Sugandha da sanyin safiya.

Rahotanni sun ce wutar gobarar ta ci gaba da ruruwa na tsawon sa’o’i.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

three + 19 =