Afrika ta Kudu na alhinin mutuwar wanda ya yaki wariyar lauyin fata Desmond Tutu

9

Ana gudanar da shirye-shiryen na mako guda a kasar Afirka ta Kudu don tunawa da rasuwar shugaban masu adawa da wariyar launin fata Archbishop Desmond Tutu, wanda ya rasu jiya yana da shekaru 90 a duniya.

Shirye-shiryen sun hada da kwanaki biyu na hutu kafin jana’izarsa a hukumance a ranar 1 ga Janairu a birnin Cape Town.

An yi ta samun sakonnin ta’aziyya daga shugabannin duniya da suka hada da Sarauniya Elizabeth ta biyu da shugaban Amurka Joe Biden da Paparoma Francis.

Desmond Tutu ya kasance daya daga cikin fitattun mutanen kasar a gida da waje.

Shugaban kasar Afirka ta Kudu Cyril Ramaphosa ya bayyana a cikin wata sanarwa cewa, Tutu ya taimaka wajen samar da ‘yantacciyar kasar Afirka ta Kudu.

Desmond Tutu, wanda ya yi zamani da Nelson Mandela, an ba shi lambar yabo ta zaman lafiya ta Nobel a shekarar 1984, saboda rawar da ya taka a fafutukar kawar da tsarin wariyar launin fata da gwamnatin tsirarun fararen fata suka kakabawa bakar fata masu rinjaye a Afirka ta Kudu daga 1948 zuwa 1991.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

2 + sixteen =