Za mu tabbatar da matasa sun zama manyan gobe – Osinbajo

25

Mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo, ya bayyana cewa gwamnatin tarayya ta dukufa wajen shirya matasan kasarnan domin fuskantar kalubalen shugabancin kasarnan a gaba.

Osinbajo ya ce za a cimma hakan ne ta wasu tsare-tsare masu zaman kansu da na gwamnati na horar da shugabanni.

Mataimakin shugaban kasar ya bayyana haka ne jiya a Legas a wajen taron shekara-shekara na kungiyar darektoci na bana.

Shugaban ma’aikatan tarayya, Folashade Yemi-Esan ce ta wakilci mataimakin shugaban kasar a wajen taron.

Osinbajo ya ce taken taron abin yabawa ne domin yana haifar da tashi tsaye ga rashin makawa a tsakanin matasa.

Ya ce bayanan da aka samu sun nuna cewa galibin ma’aikata suna tsakanin shekaru 20 zuwa 39 ne ta yadda hakan ya haifar da bukatar a yi wa matasa gyaran fuska tare da hadin gwiwa a dukkan bangarori.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

20 − three =