Masu zuba jari 70 na gida da waje sun nuna bukatar zuba jari a Jigawa

88

Kimanin masu zuba jari na gida da waje 70 ne suka nuna sha’awarsu ta zuba jari a jihar Jigawa.

Darakta Janar na masu saka hannun jari a Jigawa, Hajiya Furera Jumare ce ta bayyana haka a lokacin da take amsa tambayoyi daga manema labarai a Dutse.

Ta ce tuni masu saka hannun jari 16 suka fara aiki kuma sun zuba jarin da suka fara samun sakamako mai kyau.

Hajiya Jumare ta ce alhakinta ne jawo masu zuba jari daga ciki da wajen kasarnan su zuba jari a jihar Jigawa, wanda hakan ke haifar da da mai ido.

Ta ce kamfanoni irin su Olam da sauran kamfanonin hakar ma’adinai da masana’antu sun fara aiki a jiharnan.

Ta kara da cewa gwamnati ta bayar da filaye kyauta da hutun biyan haraji ga duk wani dan kasuwa da ke son zuba jari a jihanan.

Babban daraktar ta kara da cewa akwai kasuwar duniya ta Maigatari da ake da ita domin fitar da kayayyaki zuwa kasashen waje yayin da gwamnatin gwamna Muhammadu Badaru Abubakar ta sake kafa wata a Gagarawa, duk a kokarinta na ganin an tabbatar da aniyar ta na ganin jihar Jigawa ta kasance jihar kasuwanci mai ‘yanci da wadata.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

3 × four =