Rundunar Hisba ta jihar Jigawa ta ce ta kama karuwai 43 tare da kwace kwalaben barasa 684 a fadin jihar.
Kwamandan Hisba na jiha, Ibrahim Dahiru Garki ya bayyana haka a wata hira da manema labarai a babban birnin jihar, Dutse.
Ya ce an kama mutanen ne a yayin wani sintiri na hadin gwiwa na tsawon mako biyu tare da sauran hukumomin tsaro a garuruwa 17 na wasu kananan hukumomin jihar.
Dahiru Garki ya kara da cewa wadanda aka kama an mika su ga ‘yan sanda domin gudanar da bincike na gaskiya, daga baya a gurfanar da su a gaban kotu domin su girbe abinda suka shuka.
Ya ce ayyukan hadin gwiwa sun yi daidai da umarnin Gwamnatin Jihar Jigawa na rufe duk wasu wuraren da aka gano barasa da sauran ayyukan ash-sha a fadin jihar.
Ya yi nuni da cewa, an haramta shan barasa da miyagun kwayoyi da sauran ayyukan ash-sha a dukkan sassan jihar.