Gwamnatin Tarayya za ta rabawa ‘yan Najeriya naira dubu 5

88

Ministar kudi, kasafin kudi da tsare-tsaren kasa, Zainab Shamsuna Ahmed, ta ce gwamnatin tarayya za ta raba wa ‘yan Najeriya tallafin sufuri na naira dubu 5 a madadin tallafin mai da za ta janye gaba daya zuwa shekarar 2022.

A cewar ministar, gwamnatin tarayya za ta janye tallafin man fetur a badi kuma ta ba wa ‘yan Najeriya mafiya talauci tallafin sufuri na naira dubu 5.

Ministar ta bayyana haka a yau a wani taron Bankin Duniya kan ci gaban kasarnan, inda tace kimanin ‘yan Najeriya miliyan 30 zuwa 40, wadanda suka fi kowa talauci, za su ci gajiyar kudaden.

Zainab Ahmed ta bayyana fatan cewa kudirin dokar man fetur ta PIB ta bana da farfado da kamfanonin tace mai na gwamnati tare da sa ran bude sabbin kamfanonin tace mai masu zaman kansu a badi, zasu bunkasa cigaban tattalin arziki.

Ministar ta ce adadin wadanda za su amfana da tallafin ya dogara ne da yawan abin da ke hannu bayan janye tallafin.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

2 − one =