Gwamnatin Jigawa za ta gina masallatai 285

100

Gwamnatin jihar Jigawa ta gudanar bikin bada tayin kwangilar gina masalatan juma’a da na kamsusalawati guda 285 da gidajen hakimai da kuma kewaye makabartu a mazabun jihar 30.

Shugaban kwamitin ta yin bayar da kwangila na jiha kuma babban sakataren sashen kudi da mulki na ofishin sakataren gwamnatin jiha Alhaji Muhammad Dagaceri ya bayyana hakan a lokacin bikin bude bayar da tayin kwangilar.

Yace an bayar da kwangilar ne a matsayin ayyukan zangon farko na shekarar 2021 wanda kamfanoni 390 suka nuna shaawar gudanar da ayyukan.

A jawabinsa wakilin hukumar tantance bayar da ayyukan kwangila na jiha, Sale Abubakar ya bayar da tabbacin yin gaskiya da adalci wajen tantance kamfanonin da suka nemi aikin.

Daya daga cikin yan kwangilar Sabiu Nabakwai ya yaba wa gwamnatin jiha bisa yadda take tsaftace ayyukan bayar da kwangila a jihar.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

one + thirteen =