Gwamnatin Jigawa ta ware N50m domin gwajin HIV bisa tilas

85

Gwamnatin Jihar Jigawa ta ware sama da naira miliyan 50 domin sayen kayayyakin gwajin cuta mai karya garkuwar jiki ta HIV da ake gudanarwa bisa tilas kafin daurin aure.

Shugaban hukumar magance yaduwar cutar na jihar Jigawa, Mallam Ibrahim Almajiri, ya sanar da haka lokacin da yake kare kasafin kudin hukumar a gaban majalisar dokokin jihar Jigawa.

Yace za ayi amfani da kudaden domin samar da kayayyakin gwajin HIV na tilas domin masu shirin aure a fadin jiharnan.

Idan za a iya tunawa dai, majalisar dokokin jihar Jigawa a shekarar 2016 ta sanya hannu akan dokar da ta tilasta yin gwajin cutar HIV sau uku kafin a daura aure.

Dokar ta taimakawa jihar Jigawa wajen rage yawaitar masu kamuwa da cutar daga kashi 1.9 cikin 100 a shekarar 2014 zuwa kashi 0.3 cikin 100 a shekarar 2018.

Wata kididdiga a shekarar 2018 ta sanya Jigawa cikin jihoshi guda 3 da suka fi karancin masu cutar HIV a kasarnan.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

4 × one =