Gwamnatin Habasha ta nemi tsaffin sojoji su shiga yaki da ‘yan tawaye

37

Rundunar sojin Habasha ta yi kira ga tsoffin sojojin kasar su dawo aikin soja domin taimaka mata yaki da ‘yan tawaye.

Kiran na zuwa yayin da ‘yan tawayen yankin Tigray suka doshi Addis Ababa, babban birnin kasar.

Ofishin jakadancin kasar Amurka ya bukaci Amurkawa su gaggauta ficewa daga Habasha saboda halin tsaro da kasar take ciki.

Tun da farko gungun masu adawa sun hade kai kan manufa guda ta kawar da gwamnatin Firaminista Abiy Ahmed.

Gwamnatin kasar ta ce za ta ci gaba da fada a abinda ta kira yakin da ake yiwa tun dadewa.

Rikicin a yanzu ya shiga shekara ta biyu kuma ya raba mutane sama da dubu 400 da muhallansu, yayin da kasar ke gab da fadawa cikin matsanancin hali na yunwa.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

fifteen + thirteen =