Gwamnati za ta bibiyi aiwatar da mafi karancin albashi

15

Nan ba da jimawa ba gwamnatin tarayya za ta fara sanya ido kan yadda ake aiwatar da dokar mafi karancin albashi ta kasa ta shekarar 2019, wadda ta karawa ma’aikatan Najeriya mafi karancin albashi daga naira dubu 18 zuwa dubu 30.

Shugaban Hukumar Kula da Albashi ta kasa, Ekpo Nta, a wani taron manema labarai jiya a Abuja, ya ce hakan zai kasance hadin gwiwa tsakanin hukumomi da nufin tattara shaidun bin ka’ida da matsalolin da masu ruwa da tsaki ke fuskanta, domin samun damar bayar da shawarwari ga dukkan ma’aikata, ciki har da gwamnatoci a kowane mataki.

Ekpo Nta yace hakan zai kuma bayar da damar tsara shirin farko na dokar mafi karancin albashi ta gaba, domin dukkan masu ruwa da tsaki su san irin matsalolin da ake fuskanta domin kyakkyawan shiri.

Ya ce hukumar ta gudanar da bincike kan albashin ma’aikata a bangaren lafiya da manyan makarantun gaba da sakandare da wasu zababbun jami’o’i tare da hadin gwiwar hukumar jami’o’i ta kasa a kashi na farko.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

3 × 5 =