Buhari yace Najeriya na bukatar $1.5trn domin cike gibin ababen more rayuwa

25

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce Najeriya na bukatar dala tiriliyan 1 da rabi cikin shekaru goma, domin cimma wani matakin da ya dace a fannin gine-gine da ababen more rayuwa.

Ya ba da wannan adadi ne jiya a birnin Glasgow na Scotland a wani babban taron inganta ababen more rayuwa na duniya wanda shugaba Joe Biden na Amurka da shugaban hukumar Tarayyar Turai Ursala Von Der Leyen da Firayim Ministan Burtaniya Boris Johnson suka shirya.

Mai magana da yawun shugaban kasa, Garba Shehu, a wata sanarwa da ya fitar jiya a Abuja, ya ruwaito shugaban na cewa Najeriya a shirye take ta karbi masu saka hannun jari domin bunkasa ababen more rayuwa a kasar.

Ya kuma bayyana cewa gwamnatinsa ta dauki aikin fadada kayayyakin more rayuwa a Najeriya da muhimmanci, bisa la’akari da cewa sabbin masu saka hannun jari a sassa masu muhimmanci na tattalin arziki zasu taimaka wajen fitar da ‘yan Najeriya miliyan 100 daga kangin talauci nan da shekarar 2030.

Shugaban kasa ya yi maraba da kasashen G7 kan shirin da suka yi na samar da biliyoyin daloli na zuba jarin samar da ababen more rayuwa ga kasashe masu karamin karfi da matsakaita.

A wani labarin kuma, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi alkawarin cewa Najeriya za ta rage hayakin da take fitarwa gabadaya zuwa shekarar 2060.

Mai magana da yawun shugaban kasa, Garba Shehu, a wata sanarwa da ya fitar, ya ce Buhari ya bayyana hakan ne a jiya a lokacin da yake gabatar da jawabinsa na kasa a taron shugabanni a birnin Glasgow na kasar Scotland.

Shugaban kasar ya ce cimma burin sauyin yanayi na kasa da na duniya zai bukaci isasshen tallafi na fasaha da kudade ga kasashe masu tasowa.

Shugaba Buhari ya lura cewa saukaka samun kudaden tallafin yanayi ya zama wajibi idan aka yi la’akari da cutar corona wacce ta durkusar da tattalin arzikin kasashe masu tasowa.

Yayin da yake jawabi dangane da komawa amfani da makamashin gas a Najeriya, shugaba Buhari ya bukaci abokan huldar kasa da kasa da su samar da kudaden gudanar da ayyukan ta hanyar amfani da makamashin iskar gas a Najeriya.

Yayin da yake amincewa da cewa dena fitar da hayaki gabadaya na iya haifar da sauye-sauyen tattalin arziki a dukkan bangarori, shugaban ya ce zai bukaci samar da muhimman ababen more rayuwa.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

4 × four =