Buhari ya jajantawa wadanda rushewar gini ta rutsa da su a Lagos

16

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jajantawa iyalan da suka rasa ‘yan uwansu a wani bene mai hawa 22 da ya ruguje a Legas, yayin da har yanzu wasu ke makale.

Wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban kasa, Femi Adesina, ya fitar jiya a Abuja, ta ce shugaba Buhari ya bayyana bakin cikinsa da jama’a da gwamnatin jihar Legas, inda ya bukaci hukumomi su kara kaimi wajen ayyukan ceto.

Ya yi kira ga hukumomin daukin gaggawa da suka hada da asibitoci da su ba da duk wani tallafi da ya dace don kare rayukan wadanda aka ceto.

A wani labarin kuma, shugaban kasa Muhammadu Buhari baya goyon bayan aikata laifuka ko hukunta masu aikata laifuka a Najeriya.

Mashawarci na musamman ga Buhari kan harkokin yada labarai da wayar da kan jama’a, Femi Adesina, ne ya bayyana haka a wajen wani taron tattaunawa kan manufofin kare ‘yan jarida domin tunawa da ranar kawo karshen cin zarafin ‘yan jarida ta duniya ta bana, da aka gudanar a Abuja.

Femi Adesina ya ci gaba da cewa aikin jarida da bayyana gaskiya abubuwa biyu ne masu muhimmanci na dimokuradiyya domin daya ba zai iya rayuwa sai da daya.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

10 − 8 =