Buhari ya isa Faransa domin taron zaman lafiya

74

A yau ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sauka a birnin Paris na kasar Faransa domin halartar taron zaman lafiya na kwanaki uku na birnin Paris wanda zai gudana daga ranar 11 zuwa 13 ga watan Nuwamban da muke ciki.

Mai baiwa shugaban kasa shawara na musamman Femi Adesina ne ya sanar da hakan cikin wata sanarwa.

A cewar sanarwar, Shugaba Buhari zai kasance bako ga shugaban kasar Faransa, Emmanuel Macron kafin a fara taron zaman lafiya nan da kwanaki 2.

A wani labarin kuma, Majalisar Dattawa ta samu bukatar shugaban kasa Muhammadu Buhari na amincewa da Farfesa Ayo C. Omotayo a matsayin Darakta-Janar na Cibiyar Nazarin Siyasa da Dabaru ta kasa.

A cewar wata sanarwa da Ezrel Tabiowo, mai magana da yawun shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan, ya fitar, ya ce bukatar na kunshe ne a cikin wata wasika da Ahmad Lawan ya karanta yau, jim kadan bayan da majalisar ta dawo zamanta daga hutun kwanaki 18 da ta yi.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

18 + ten =