Ambaliyar ruwa ta shafi mutane miliyan 1 a Sudan ta Kudu

141

Gwamnatin Kasar Sudan Ta Kudu ta ce sama da mutane miliyan daya ne ambaliyar ruwa ta shafa a kasar a daminar bana.

Ministan agajin gaggawa da kula da annoba na kasar, Peter Mayen ne ya sanar da hakan yayin da yake karbar tallafin kayan abinci daga gwamnatin kasar Masar.

Yace za a rabar da kayan abincin da aka kawo da suka hada da sikari da shinkafa da sauran kayayyakin ga mutanen da annobar ta shafa.

Gwamnati kasar Masar ta kai tallafin tan 12 na kayan abinci a jirgin sama.

A makon jiya ne, ofishin da ke lura da ‘yan gudun hijira na majisar dinkin duniya ya rawaito cewa ambaliyar ta shafi mutane dubu 76 a kasar.

Amma daga baya gwamnati ta ce adadin wadanda abin ya shafa ya kai miliyan 1 da dubu dari biyu.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

seven − 7 =