Majalisar Dinkin Duniya ta tabbatar da cewa an shafe kwanaki ana gwabza fada tsakanin kabilu a yankin Darfur na kasar Sudan wanda yayi sanadiyyar mutuwar mutane akalla 43 tare da raba dubbai da muhallansu.
Rikicin ya barke ne a makon jiya tsakanin Larabawa makiyaya da manoma daga kabilar Misseriya Jebel a garin Jebel Moon dake yammacin Darfur.
Majalisar Dinkin Duniya ta ce sama da kauyuka 40 ne aka kona tare da wawashe kayayyaki a rikicin.
Majalisar ta kara da cewa mutane da dama sun bace ciki har da yara kanana.
Ana yawan samun barkewar tashin hankali a yankin Darfur tun bayan sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya a karshen shekarar da ta gabata, wanda ya kai ga janyewar dakarun wanzar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya.