‘Yansanda sun kama makiyayi da ‘yan damfara a Jigawa

147

‘Yansanda a jihar Jigawa sun kama wani makiyayi dan shekara 25 wanda ake zargi da kutsawa cikin wata gona tare da lalata amfanin gona na kudinsu ya kai sama da naira dubu 200 a kauyen Takatsaba dake karamar hukumar Sule Tankarkar.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yansanda a jiharnan, Lawan Shiisu Adam, ya tabbatar da kamen cikin wata sanarwa da ya fitar jiya a Dutse.

Yace ‘yansanda sun kuma kama shanunsa guda 73 da tumakansa 13 wadanda suka shiga cikin gonar a ranar 10 ga watan Oktoban da muke ciki.

Shiisu Adam yayi nuni da cewa ba a samu asarar rai ba a lamarin, inda ya kara da cewa an samu shawo kan matsalar.

Yace ana cigaba da bincike kan lamarin kuma ana kokarin kama wasu da ake zargi wadanda suka arce.

A wani labarin kuma, rundunar yansandan jihar Jigawa ta kama wani mutum mai shekaru 31 mai suna Abdullahi Maikudi da wani mai suna Sirajo Habibu bisa zargin damfarar wasu masu hulda da banki a Dutse.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yansanda a jiharnan, Lawan Shiisu Adam, ya tabbatar da kamen wadanda ake zargin jiya a Dutse.

Yace kamen ya biyo bayan korafin da wadanda aka damfarar suka shigar a ranar Laraba cewa wani mai suna Abdullahi ya damfare su bayan sun je wani banki a Dutse domin cire kudi ta ATM, inda ya nuna zai taimake su.

Shiisu Adam yace wanda ake zargin ya sauya musu lambobin sirri inda ya cire kudi naira dubu 50 da naira dubu 8 daga asusu 2 na jiya.

Ya kara da cewa yansanda sun samu nasarar kama wanda ake zargin, wanda daga baya ya ambaci Surajo Habibu na unguwar Limawa dake karamar hukumar Dutse, a matsayin abokin aika-aikarsa.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

9 − 8 =