Wadanda ake zargin ‘yan IPOB ne sun kashe jami’an tsaro 175

28

Gwamnatin Tarayya tace bincikenta ya nuna cewa ‘yan awaren kungiyar IPOB da aka haramta, ya zuwa yanzu sun kai hari kan ofishoshin yansanda 164 a fadin jihoshi daban-daban.

Gwamnatin tarayya ta kara da cewa ‘yan awaren dauke da makamai sun kashe jumillar jami’an tsaro 175.

Matsayar gwamnatin tarayyar na kunshe cikin wata sanarwa da babban lauyan tarayya kuma ministan shari’ah, Abubakar Malami, ya fitar a yau.

Gwmanatin tarayyar ta kuma ce wadanda ake zargin yan kungiyar ta IPOB ne sun kaddamar da hare-hare 19 akan gine-gine hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa, INEC, lamarin da ya jawo kone motoci 18.

A wani labarin kuma, ‘yan bindigar da ake zargin ‘yan kungiyar IPOB ne, sun cinna wuta kan fadar sarkin kauyen Etekwuru a jihar Imo.

Kazalika, an kone motarsa tare da wasu kayayyaki a lokacin harin. Majiyoyi sun ce lamarin ya auku a jiya da dare.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

eight + three =