Sojoji sun yi juyin mulki a Sudan

10

A yau ne wasu gungun sojoji da ba a san ko su wanene ba suka tsare mukaddashin Firai Ministan Sudan, Abdallah Hamdok.

Matakin da aka dauka kan Hamdok ya biyo bayan kamen da sojojin suka yiwa manyan jami’an fararen hula da suka hada da ministocin gwamnati, da mai bayar da shawara kan harkokin yada labarai na Firayim Minista da wani dan majalisar koli dake mulkin kasar.

Ma’aikatar yada labarai ta kasar ta ce kwacen mulkin na sojoji ya kuma zo tare da katse layukan sadarwa da dakile intanet da kuma toshe gadoji a Khartoum babban birnin kasar, ta mai bayyana matakan a matsayin juyin mulki.

Wadanda aka tsare sune ministan masana’antu da ministan yada labarai da wani dan majalisar koli da mai bayar da shawara ga firayim ministan kasar.

Dubunnan masu zanga-zanga sun cika titunan Khartoum da birnin Omdurman don nuna rashin amincewa da kwacen mulkin sojojin.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

17 + nineteen =