Sarkin Dutse ya bukaci a sake fasalin manhajar koyar da malamai

125

Mai martaba sarkin Dutse, Dr Nuhu Muhammad Sanusi, ya kalubalanci tsangayoyin ilimi a manyan makarantu da su sake fasalin manhajar karatunsu zuwa samar da malamai da za su samar da dalibai masu inganci.

Da yake jawabi a wajen bukin bude wani taro na kwanaki uku da sashen ilimi na jami’ar tarayya ta Dutse ya shirya, sarkin wanda ya samu wakilcin Danmasanin Dutse, Alhaji Adamu Aliyu Kiyawa, ya danganta koma bayan ilimi ga rashin kyawun koyo da koyarwa, duk da kasancewar akwai masana da yawa.

Mataimakin shugaban jami’ar, Farfesa Abdulkarim Sabo Mohammed, a nasa jawabin, ya ce jami’ar a shirye take ta hada gwiwa da hukumomin da abin ya shafa don ciyar da koyo da koyarwa, gaba a jami’ar.

Shugaban tsangayar ilimi na Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zaria, Farfesa Haladu Bayero, ya bayar da shawarar sake fasalin manhajar koyar da ilimin malanta, domin dacewa da abin da ake bukata da nufin sanya fasaha a harkar koyo da koyarwa a wannan karnin na 21.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

one × 5 =