Kungiyoyin da ke goyon bayan Iran sun yi watsi da zaben Iraqi

51

Jam’iyyun da ke goyon bayan kasar Iran da kungiyoyi masu dauke da makamai sun yi watsi da sakamakon farko na zaben kasar Iraki wanda suka kira magudi da zamba cikin aminci.

Zaben ‘yan majalisa na ranar Lahadi, na biyar a kasar da ke fama da yaki tun bayan mamayar kasar Amurka da kifar da gwamnatin Saddam Hussein a shekarar 2003, ya kasance mafi karancin fitowar jama’a da kashi 41 cikin dari.

Dangane da sakamakon farko daga hukumar zaben kasar, babban jam’iyyar da tayi nasara ita ce ta malamin addini kuma mashawarcin siyasa Muqtada al-Sadr, wanda ya samu karin kujeru zuwa 73 daga kujeru 329 na majalisar.

Jam’iyyun da suka yi asarar kujeru sune na masu goyon bayan kasar Iran, wadanda da ke da alaka da kungiyoyin masu dauke da makamai da suka hada da kungiyar mayakan da aka fi sani da Hashd al-Shaabi.

Jam’iyyar Kawancen Fateh, wacce a baya ita ce ta biyu mafi karfi a majalisar, ta sami koma baya sosai daga kujeru 48 zuwa kusan kujeru 12.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

1 × three =