Iyorchia Ayu ya zama dan takarar shugabancin PDP da aka zaba

65

Tsohon Shugaban Majalisar Dattawa Iyorchia Ayu ya zama dan takarar kujerar shugaban jam’iyyar PDP na kasa.

Zabin nasa ya zo ne bayan wani zaman ganawar ‘ya’yan jam’iyyar PDP na Arewa wanda aka yi a gidan gwamnan jihar Bauchi dake unguwar Asokoro dake Abuja.

A wani labarin kuma, Jam’iyyar PDP a jihar Zamfara a yau ta koka kan shirin rusa helkwatarta ta jiha, wanda hukumar tsare-tsaren birane da yankuna ta jihar Zamfara ke shirin yi.

Sakataren Yada Labaran jam’iyyar a jihar, Alhaji Farouk Ahmad Shattima, ya shaidawa manema labarai cewa bayan gwamna Bello Mohammed Matawalle ya koma jam’iyyar APC, an karbe helkwatar PDP inda aka yi mata fenti da tambarin APC.

Sai dai, ba a samu damar jin ta bakin jami’an hukumar tsare-tsaren birane da yankuna ta jihar Zamfara ba, har zuwa lokacin da ake hada wannan labarin.

A dai jam’iyyar PDP, tsohon gwamnan jihar Jigawa, Alhaji Sule Lamido, ya yi fatali da amincewar da majalisar dattawa ta yi a wani kudirin dokar gyara zabe wanda ya bayar da umarnin gudanar da zaben kato bayan kato domin zaben ‘yan takarar da jam’iyyun siyasa za su tsayar.

Sule Lamido, wanda dan Jam’iyyar PDP ne, ya ce umarnin ya sabawa Kundin Tsarin Mulkin Najeriya kuma ya shawarci jam’iyyarsa ta kalubalanci matakin a kotu.

Majalisar dattawa, a ranar Talata, ta amince da sashin bayan ta canja matsayinta na farko don yin yarjejeniya tare da Majalisar Wakilai kan tsayar da ‘yan takarkarun jam’iyyu a zabe.

A wata sanarwa da ya fitar jiya, Sule Lamido ya ce Kundin Tsarin Mulki ya bai wa jam’iyyun siyasa damar tsara yadda ake gudanar da al’amuransu kuma ya umarci Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) da ta tabbatar sun bi ka’idojin kundin tsarin mulkinsu.

Sule Lamido ya ce majalisar kasa, wacce ke karkashin ikon jam’iyyar APC, ta mayar da kanta a matsayin mai kula da jam’iyyun siyasa.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

9 + twelve =