Hukumar Cigaban Fasahar Fasahar Sadarwa ta Kasa NITDA, karkashin Darakta Janar Mallam Kashif Inuwa Abdullahi, ta horas da mata ‘yan jarida su 50 da aka zabo daga jihoshin Arewa maso Yamma kan aikin jarida na zamani kuma ta raba kwamfutoci 50 ga mahalarta taron da nufin kara musu kwarin gwiwar rungumar fasahar zamani a sana’arsu.
Taron bita na kwana biyu da aka gudanar a Otal din 3 Star dake birnin Dutse a nan jihar Jigawa, karkashin inuwar kungiyar mata ‘yan jarida ta kasa, reshen jihar jigawa, ya samu halartar darakta janar na hukumar ta NITDA, wanda Bashir Ibrahim ya wakilta.
Da yake bude taron bitar, Bashir Ibrahim ya bayyana cewa manufar horon shine koyawa mahalarta taron hanyoyin amfani da fasahar sadawar a aikin jarida da nufin kawo sauyi a sana’arsu, musamman a tsakanin mata ‘yan jarida. A jawabinta na bude taron, shugabar kungiyar mata ‘yan jarida ta kasa reshen jihar Jigawa, Hajiya Hauwa Ladan, ta yaba da kokarin Mallam Kashif Inuwa Abdullahi.