Gwamnatin Zamfara ta samu ceto mutane 200 da aka sace

39

Gwamnatin jihar Zamfara a jiya ta ce ta tabbatar da sakin akalla mutane 200 da ‘yan bindiga suka sace ta hanyar tattaunawar zaman lafiya da daukan sauran matakan tsaro.

Kakakin Majalisar Dokokin jihar Zamfara, Alhaji Nasiru Magarya ne ya bayyana hakan a Gusau yayin da ya karbi bakuncin kungiyar  Shugabannin Majalisun Jihohin kasarnan, wanda suka kai masa ziyarar ta’aziyya bisa rasuwar mahaifinsa, Alhaji Mu’azu Magarya.

Mahaifin kakakin, wanda aka yi garkuwa da shi a watan Augusta, ya mutu yayin da yake hannun ‘yan bindiga bayan ya shafe makonni a hannunsu.

An yi sallar jana’iza ga mamacin ba tare da gawarsa ba, kasancewar ba a karbota daga hannun ‘yan fashin dajin ba.

Tawagar karkashin jagorancin kakakin majalisar dokokin jihar Bauchi kuma shugaban kungiyar, Abubakar Y. Sulaiman, ta kunshi kakakin majalisar dokokin jihoshin Kano da Katsina da Yobe.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

12 + 8 =