Gwamnatin za ta raba tukunyar gas na girki 774,000

29

Gwamnatin tarayya ta kammala shirye-shiryen fara rabon tukunyar gas ta girki guda dubu 774 ga mata a yankunan karkara.

Ministar harkokin mata, Pauline Tallen, ta sanar da haka a wajen taron ranar girkin da babu hayaki da aka gudanar a Abuja, inda ta bayyana cewa kowace karamar hukuma a kasarnan za ta samu tukunyar gas guda dubu 1 a matsayin wani bangare na habaka girkin da babu hayaki.

Pauline Tallen ta kara da cewa manufar shirin shine fadakarwa, ilimintarwa da wayar da kai dangane da amfani da makamashin girkin da ba na itace ba domin mata, da nufin inganta lafiya da walwalar matan karkara.

Tace an kaddamar da kashin farko na rabon a jihoshin Adamawa, Edo, Ekiti, Ebonyi, Katsina, Nasarawa da Babban Birnin Tarayya.

Ta kara da cewa za a fara kashi na biyu na rabon a jihoshin Akwa Ibom, Gombe, Bauchi, Plateau, Niger, Sokoto, Kebbi, Bayelsa, Kwara, Jigawa, Oyo, Osun, Enugu, Imo da kuma Delta.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

12 − 3 =