Gwamnatin Tarayya ta yi barazanar rushe gidaje

21

Gwamnatin tarayya ta yi barazanar rushe gidajen da aka gina a kusa da gabar koguna da tekuna a fadin kasarnan.

Ministan sufuri, Chibuike Rotimi Amaechi, ya sanar da haka a jiya a wajen bikin ranar ma’aikatan ruwa ta bana.

Yace gwamnatocin jihoshi da daidaikun mutane basu da damar mallakar ruwa, sayarwa ko bayar da filaye ga kowane mutum ko gungun mutane da nufin gina gidaje a gabar ruwa.

Yayi bayanin cewa gwamnatin tarayya ce kadai take da wannan damar, ban da gwamnatocin jihoshi.

Yace gwamnatin tarayya zata yanke shawarar lokacin da zata rushe gidajen da aka gina a tsakiyar ruwa ko a gabar ruwa.

Shima da yake jawabi, manajin darakta na hukumar kula da tashoshin jiragen ruwa ta kasa, Mohammed Bello Koko, yayi alkawarin inganta jin dadi da walwalar ma’aikatan ruwa.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

2 × 4 =