Gwamnatin Mali ta kori wakilin ECOWAS daga kasar

22

Gwamnatin Kasar Mali ta kori wakilin kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afrika ECOWAS a kasar, a daidai lokacin da ake kara matsa mata lamba kan ta sanar da takamaiman lokacin mika mulki ga farar hula.

Ma’aikatar harkokin wajen kasar ta gayyaci Hamodou Boly tare da sanar masa da matakin da gwamnati ta dauka na korarsa.

Kasar Mali dai tana takun saka tsakaninta da kungiyar ta ECOWAS kan bukatar gudanar da zabe a watan Fabrairu.

An dakatar da kasar daga kungiyar ta ECOWAS a watan Mayu bayan shugaban rikon kwaryar kasar, Kanar Assimi Goïta, ya yi juyin mulki karo na biyu cikin kasa da shekara guda.

Firayim Ministan kasar, Choguel Maïga ya nuna cewa za a iya jinkirta zaben, saboda damuwa kan sahihancinsa.

Akwai fargabar yadda sojojin Mali suke tsoma baki a rikicin siyasa, lamarin dake cigaba da kawo cikas wajen magance matsalar tsaro da ta addabi yankunan arewa da na tsakiyar kasar.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

20 − 8 =