Gwamnatin Jigawa ta hada kai da direbobi 600 domin daukar masu nakuda

18

Hukumar kiwon lafiya matakin farko ta jihar Jigawa ta kulla yarjejeniya da masu motoci sama da 600 don jigilar mata masu juna biyu zuwa duk wani asibiti da ke kusa.

Daraktan hukumar, Dr Abdulqadir Yakubu ne ya bayyana hakan yayin wani taro a karamar hukumar Kiyawa da kungiyar Save the Children International ta shirya a Kwalejin Gwamnatin Tarayya dake Kiyawa.

Dr Yakubu ya ce kungiyar Save the Children International karkashin shirin INSPIRING za ta tallafa wa shirin kuma an shigar da da yara ‘yan kasa da shekaru biyar dake bukatar da duk wani daukin gaggawa.

A cewarsa, a karkashin shirin, mazauna al’umomi ne suka zabo masu motocin kuma gwamnati ta tantance su.

Ya ce gwamnatin jihar tana da kudade na musamman a asusun hukumar don wannan aikin, kuma za a rika biyan masu motocin kowane wata gwargwadon yawan jigilar da suka yi.

A wani labarin kuma, gwamnatin jihar Jigawa tace ilimintar da makiyaya na taka muhimmiyar rawa wajen magance dayawa daga cikin kalubalen rashin tsaro a kasarnan.

Kwamishinan ilimi, kimiyya da fasaha na jiharnan, Dr. Lawan Yunusa Danzomo, ya sanar da haka yayin taro da manema labarai da aka gudanar a Dutse.

Yace gwamnatin jihar ta lura cewa makiyaya suna fuskantar karancin samun ilimi ta hanyar tsarin ilimin bai daya, lamarin dake jawowa su fara shaye-shayen miyagun kwayoyi da ayyukan ta’addanci.

Kwamishinan yayi nuni da cewa ana shirye-shiryen kafa sabbin kananan makarantun sakandire guda 10 domin al’ummar makiyaya, da nufin sanya daliban da suka kammala makarantun firamare.

Ya kara da cewa an kuma kafa cibiyoyin ilimin manya guda 164 domin ilimantar da makiyaya magidanta akan yadda zasu gudanar da addini da kuma yadda zasu sansanta rikici tsakaninsu cikin ruwan sanyi.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

5 × 2 =