Gwamnati za ta biya tallafin mai a watanni 6 na farkon 2022

11

Gwamnatin tarayya ta ce za ta cigaba da biyan tallafin man fetur a cikin watanni shida na farkon shekara mai zuwa ta 2022.

Ministar kudi, kasafin kudi da tsare-tsaren kasa, Zainab Shamsuna Ahmed ta bayyana hakan a wani zama da aka gudanar a taron tattalin arzikin kasa da ke gudana a Abuja.

Ta ce gwamnatin tarayya ta yi tanadin tallafin man fetur har zuwa karshen watan Yuni na shekara mai zuwa, inda ta kara da cewa za a fara aiwatar da janye tallafi gabadaya a harkokin mai fetur da iskar gas nan da watan Yulin badi.

Shugaban majalisar bayar da shawara kan tattalin arziki, Doyin Salami, ya ce ya dade yana muhawara kan batun tallafin mai.

Ya kuma ce sabuwar dokar masana’antar man fetur ta PIA ta haramta biyan tallafin man fetur.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

five × four =