Wata gobara da ta tashi a wani gini da ke kudancin birnin Taiwan ta kashe akalla mutane 46 tare da jikkata wasu 41.
Gobarar a ginin mai hawa 13 ta tashi ne da sanyin safiyar yau kuma an dakile ta da kusan wayewar gari.
Wadanda suka shaida lamarin sun shaidawa kafafen yada labarai na cikin gida cewa sun ji karar fashewar wani abu da misalin karfe uku na daren yau.
Sanarwar da hukumar kashe gobara ta birnin ta fitar ta ce bayan kammala bincike kan ginin mai shekaru 40, sun iya tabbatar da mutuwar mutane 46.
Ta kuma ce gobarar ta yi karfi sosai kuma ta lalata benaye da yawa.
Shugaban hukumar kashe gobarar, ya shaidawa manema labarai a wurin cewa akalla gawawwaki 11 aka aika kai tsaye zuwa dakin ajiye gawa.
Wasu mutane 14 da ba su nuna alamun rayuwa ba, na daga cikin 55 da aka kai asibiti.