El-Rufa’i ya gabatar da kasafin kudin badi na N233bn

10

Gwamna Nasir El-Rufai ya gabatar da daftarin kasafin kudin badi na naira biliyan 233 ga majalisar dokokin jihar Kaduna.

Kasafin kudin yana da naira biliyan 146 na manyan ayyuka da kuma naira biliyan 87 da miliyan 600 na gudanar da gwamnati.

Da yake magana a yau yayin gabatar da daftarin kasafin kudin, El Rufa’i ya yi nuni da cewa rabe-raben da aka yi a kasafin kudin na badi, sun yi daidai da demokradiyya da ka’idojin shugabanci wanda a koda yaushe suke jagorantar kasafin kudi 6 na baya da gwamnatinsa ta gabatar.

Da yake karin haske kan kasafin kudin na naira biliyan 233, gwamnan ya bayyana cewa manyan ayyuka sun dauki kashi 63 yayin da bangaren gudanar da gwamnati yake da kashi 37 ciki 100.

Nasir El Rufa’i ya ce kasafin kudin badi ya haura kasafin kudin bana na naira biliyan 237 da miliyan 520.

Ya cigaba da cewa bangarorin da aka sanya a gaba a kasafin kudin sun hada da Ilimi da lafiya da ababen more rayuwa, kamar yadda yake a kasafin kudin shekarun baya.

A halin da ake ciki, an yi garkuwa da wasu daliban makarantar St. Albertine Seminary School, Fayit dake Fadan Kagoma a karamar hukumar Jema’a ta jihar Kaduna.

Wata majiya daga Fadan Kagoma ta shaidawa manema labarai cewa masu garkuwa da mutanen sun kutsa cikin kwalejin da misalin karfe 10 na daren jiya, inda suka rika harbi kan mai uwa da wabi.

Majiyar ta ce masu garkuwar sun yi garkuwa da wasu malaman makarantar da har yanzu ba a san inda suke ba.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sanda a Kaduna, ASP Muhammed Jalige, bai amsa kira ko mayar da martanin sakon da aka aika masa zuwa wayarsa ba.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

fifteen − twelve =