Buhari ya bayar da umarnin janye haramcin amfani da Twitter

52

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya ce dole ne Twitter ta cika sharuddan gwamnatin tarayya 5 kafin a dage dakatar da shafin.

Shugaban kasar ya fadi haka ne yau yayin watsa jawabinsa ta gidan talabijin don murnar cikar Najeriya shekaru 61 da samun ‘yancin kai.

Ya lissafa sharuddan da suka hada da cewa dole ne kamfanin Twitter ya kula da tsaron kasa da hadin kan kasa da rajista, bude ofishinsa tare da wakilci a Najeriya; da sasanta rikici da sauransu.

Gwamnatin Tarayya ta dakatar da ayyukan Twitter a watan Yuni bayan shafin ya goge wani sakon Twitter mai cike da cece-kuce da Shugaba Buhari ya wallafa.

Da yawa daga cikin ‘yan Najeriya, masu fafutuka da sauran kasashen duniya sun yi Allah wadai da dakatarwar a matsayin tauye ‘yancin fadin albarkacin baki.

Ministan yada labarai, Lai Mohammed, kwanan nan ya ce tuni Kamfanin Twitter ta cika manyan bukatun gwamnatin tarayya kuma za a dage dakatarwar nan ba da jimawa ba.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

19 − 10 =